LOAPI VIRUS!
Masu bincike akan harkar tsaro ko kuma security na computer, sun binciko wata sabuwar Virus da ke kama wayoyi kirarAndroid. Wannan sabuwar Virus ana kiranta da “Loapi” virus, kuma tana da matukar hatsarin gaske.
Ita dai wannan Virus ta fara baiyanuwa a cikin wannan makon, kuma ya zuwa yanzu ta kama dubban wayoyin kirar android. Masu bincike a kamfanin nan da ya kware a fagen samar da Antivirus mai suna Kaspersky, su ne suka bayyana labarin gano wannan Virus. Wadannan masu bincike sun bayyana wannan Virus a matsayin wata abu da da za’a iya alakantawa da “komi da ruwanka” domin kusan duk wata barna da aka sani Virus na yi a cikin wayoyin android, to ita ma wannan Virus tana yinsu.
Ita wannan Virus idan ta kama waya to zata sanya duk wasu application da ke cikin wayar su bar aiki tare da yi ma wayar rooting, a lokaci guda kuma ta rika zuke wuta ko kuma power din wayar, wannan kan sanya wayar dau zafi sosai ta yanda kai tsaye batirin kan iya mutuwa ko kuma wayar ta yi bindiga!
Akwai wasu muhimman aiyuka da wannnan Virus ke tilastawa waya yinsu. Wadannan ayyuka sun hada da:
1. Hakar kudin sama (wato Bitcoin mining), ta yanda masu ita zasu samu wadannan kudaden
2. Yin amfani da wayar domin yin hacking din wata computer, ta yanda ko da aka yi binciken wanda yayi hacking din, to sunan mai wayar za’a gani a maimakon su hackers din
3. Sanya tallace-tallace masu yawa a kan screen
4. Yin leken asiri akan sakonnin mutum (SMS)
Wadannan muhimman aiyuka da wannan Virus ke sanyawa waya na yi duk a cikin lokaci daya, su ke sanya wayar ta dauki zafi sosai har ma batirin ya iya yin binda.
Wasu dubaru da masu wannan Virus din ke amfani da su domin yaudarar mutum yayi installing wannan App na su sun hada da nuna wannan App din a matsayin wani app mai dauke da hotunan banza, da kuma sanya App yayi kamanceceniya wasu application da aka fi amfani da su.
TA YAYA ZAKU IYA KAREN KANKU DAGA “LOAPI” VIRUS?
Idan wannan Virus bata kama wayarku ba, to abin da zaku yi domin kare kanku shine kada ku sake ku yi installing wani application da bai fito daga sahihin wuri ba (misali Play Store).
Idan kuma an samu rashin sa’a wannan Virus ta kama wayarku, to abin yi shine kawai mutum yayi kokarin zare batirin wayar zuwa wani lokaci, tare da yin wiping ko kuma goge abubuwan da cikinta gaba daya!
Da fatan za’a kula sosai domin kare kai daga wannan hatsabibiyar Virus.

KASHI 70% CIKIN MUTANE MASU AMFANI DA KAFAR SADARWA NA FUSKANTAR BARAZANAR DANDATSANCI(HACKING)
Akwai da yawa saga cikin mutane yanzu wadanda basu San muhimmancin password din suba.Wasu mutanen kuma duk da cewa sun san muhimmancin password din, to amma kuma ga dukkan alamu basu san hatsarin da ke tattare da barin wani ya san password din su ba. Na fara wannan kasida da wannan zance ne saboda yanda muka ga mutane na yi ma password rikon sakainar kashi, sai ka ce baya da wani amfani. Wannan halin ko in kula ne ya sanya sama da 70% na mutanenmu ke fuskantar barazanar hacking na computer ko wayoyinsu ko kuma account din su. A cikin wannan kasidar, zan yi tsokaci ne akan barazanar Hacking da mafi yawancin mutane ke fuskanta, musamman masu mu’amala da dandalin sada zumunta na Facebook.
Password dai wata hikima ce da ake amfani da ita a duniyar computer domin samar da tsaro akan wani bayani ko kuma bayanai da ke da alaka da wani mutum, gungun mutane, kamfani, gwamnati da dai sauransu. Ana amfani ne da password musamman domin baiwa bayanan sirri kariya daga bata gari ko kuma wasu da ba’a bukatar su ga wadannan bayanan. Saboda wannan dalili ne ya sanya ake son password ya kasance yana da karfin gaske ta yanda ba za’a iya hasasoshi ko kuma guessing din sa ba. Wadanda suka san mi ake nufi da hacking sun san cewa akwai dubaru kala-kala da ake amfani da su waje ganowa ko kuma breaking din password na computer ko kuma shafin internet da karfin tuwo.
Sanin kowa ne a wannan zamani da muke ciki, duk wanda ya samu password dinka (kamar na computer ko Facebook) to kamar ya samu makullin gidanka ko kuma dakinka ne, domin samun wannan password naka zaya bashi dama ya samu ganin duk wasu bayanai wadanda kake boyo da ma wadanda baka boyewa.
A lokutan baya da suka gabata, bincike ya nuna cewa mutane a wancan lokacin suna amfani da wasu kalmomi kamar sunansu, ranar haihuwarsu, lambar waya, da dai sauransu wajen sanya password dinsu. Mutane a wancan lokaci suna yin haka ne domin gudun kar su manta wannnan password na su. Amma bayan wani dan lokaci sai aka gano cewa masu kutse ta computer da internet ( Hackers) suna amfani da wannan dama wajen yi ma mutane kutse ko kuma hacking a computocinsu da kuma shafukansu na internet, ta hanyar amfani da wadannan sunaye ko kuma ranaku da suke amfani da su wajen sanya password din su. Wannan ne ya sanya dole mutane suka bullo da wasu dubarun sanya password saboda sun gano cewa hackers na amfani da wannan sakakin da mutane ke da shi, na rashin amfani da password mai karfi wajen yi musu ta’annati. Wannan dubaru da mutane suka bullo da su sun hada da amfani da wasu lambobi daban wadanda ba lambobin wayoyinsu ba da kuma wasu kalamai wadanda ba sunayensu ne ba, amma dai wani abu ne da zasu iya tunawa cikin sauki. Da ganin haka, sai su ma hackers suka bullo da wasu dubaru kala-kala wadanda suka hada da Brute force ,
Dictionary Search da dai sauransu. Wadannan dubaru ana amfani da su ne wajen breaking ko kuma karya password da karfin tuwo!
Amma kuma binciken baya-bayan nan ya gwada cewa, wadannan dubaru da hackers ke amfani da su suna da iyaka. Wannan iyaka ta su itace, suna gano password ne kawai wanda ke dauke da lambobi zalla ko kuma kalmomi zalla. Wannan ya nuna cewa mafi yawancin wadannan dubarun na hackers basu iya breaking din password wanda aka hada shi ta hanyar hadawa ko kuma combination na lambobi da kuma bakake. Wannan ne ya sanya a ko da yaushe masana ke shawartar mutane su tabbatar cewa sun yi amfani da lambobi da kuma bakake (letters) wajen hada password na su, domin irin wannan password yana da wuyar gaske wani ya iya hasashensa (guess) ko kuma ayi amfani da wata karamar hikima wajen gano shi.
Wannan dabi’a ta amfani da lambobin waya ko ranar haihuwa, ko kuma sunaye wajen sanya password, tuni hackers sun rigaya sun gano hanyoyin da zasu bi domin kauce musu (Bypass). Da fatan duk wanda ya karanta wannan kasida zaya sauya yanayin password din sa domin kare kanshi daga kutsen hackers
No comments:
Post a Comment