ANDROID

ABUBUWAN DA MUKE YI WADANDA KE BATA MANA WAYOYIN ANDROID DA BAMU SANIBA.

Dayawa saga cikin mutane idan wayarsu ta lalace sai su zargi companies na wayoyinsu, mutane na ganin laifin company na warne ne da bai ingantataba.Alhali kuwa yawanci mune muke janyo matsalar.
Ganin hakane yasa na rubuta wannan kasidar akan wasu abubuwa da muke yi wadanda ke janyowa wayoyinmu matsaloli:


1. Saukarda (Download) "application" Daga Kowanne Shafi Na Yanar Gizo.
Mafi yawan masu wayar hannu kirar android na da dabi'ar saukar da wasu "application" da suke ganin zai musu amfani imma a lokacin ko kuma nan gaba. Sai dai abin da ba sa la'akari da shi, shine tantancewa tare da sanin sahihancin shafin da za su saukar da wadannan abubuwa.
Babban abin da ake tsoro shine idan akai rashin sa'a sai wayarka tai aragama da "Virus", kuma kowa ya san illar da hakan zai haifarwa wayarsa.
Mafita anan shine saukar da irin wadannan manhajoji daga shafuka marasa hadari, ko dai saboda ficen da su kai, ko ta hanyar binciken sahihancinsu, ko samun sahihin labari daga wani wanda ya gano hakan.
2. Kira Ko Amsa Shi Yayinda Waya ke Caji.
Wasu da yawa ba su da masaniyar cewa yin kira ko amsa shi na da hadari ga lafiyarsu ko ita kan ta wayar. Don haka yana da kyau ka guji amfani da ita a lokacin da ka makala ta a caji, musamman kira ko amsa kiran ko kuma yin gem da ita.
Hakan zai zama kamar ba wata damuwa a gare ka, amma fa al'amarin ba haka ya ke ba. Abu mafi kyau shine kaucewa hakan a duk lokacin da wayarka ke caji.
Abu na gaba shine ajiyewa wayarka a inda ba za ta dauki zafi ba, don haka ka iya janyo mata wata matsalar da ba'a tsammmanin ta.
3. Cusa Wayar Android A Matsattsen Aljihu.
Duk wani mai amfani da wayar android ya san yadda ta ke wajen samun lahani daga faruwar karamin abu, wannan dalili ya sa cusa ta a aljihu mai matsi kan iya haifar mata da matsala.
4. Ajiye Wayar Android Karkashin Matashin Kai Yayin Barci.
Wannan ma wata gaba ce mai matukar hadari ga wayarka. Ta yiwu ka danne ta ko kuma idan gadon da ka ke kwance yana da tudu ka turo ta kasa ba ka sani ba. Kowa yasan yadda wayar android ke samun matsala idan ta fado, wani lokacin ma ko ba daga waje mai bisa ba ne.
Abin da ya fi dacewa aduk lokacin da ka zo barci sai ka kashe wayarka, ka adana ta a waje mai kyau da zai kare ta daga fadowa.
5. Kusantar Da Ita Ga waje Mai danshi.
Mun sani ruwa ko danshi na da hadari ga akasarin na'urorin da ke aiki da lantarki, kuma haduwarsu da ruwan ko damshin kan haifar mu su da matsala. Kamar haka ne ita ma android ka iya samun matsala matukar tai arangama da ruwa ko wani damshi mai yawa da zai iya ratsa ta.
Don samun ingancin wayar android sai ai duk abin da za'a iya don nesantar da ita daga wannan yanayi.
6. Yin Cajin Android Fiye Da Kima.
Wasu kan yi tsammanin barin wayarsu ta jima a caji, shi zai sa ta zuki cajin da yawa yadda kuma za ta jima da shi ba tare da ya kare ba. Sai dai al'amarin ba haka ya ke ba. An kero ta ne da tsarin idan batir ya nuna ya cika to haka abin ya ke. Barin ta a wuta ba wani abu da zai kara sai dai lahani ga wayar musamman batir din.
7. Yawan Barin Waya Ta Mutu Sakamakon Rashin Cajin.
Sau da yawa akan samu wasu da ke barin cajin wayarsu ya kare karkaf, wanda yin hakan ba karamin lahani ke haifarwa da wayarsu ba, alhali su ba su sani ba. Don samun tsawon ran android a guji barin cajinta ya kare kwata kwata.

No comments:

Post a Comment