YANDA AKE AMFANI DA TSARIN D.N.D A WAYAR SALULA.
Mafi yawancin mutane masu fama da matsalar satar kudi ko kuma dibar musu kudi daga cikin layukan wayoyinsu ba tare da saninsu ba, sun san cewa ana iya tsaida wannan matsalar ta hanyar aikawa da sakon
STOP zuwa 2442 . Aika wannan sako na
STOP zuwa ga 2442 zaya baka damar tsaida karbar sako daga lambar da ake dibar maka kudi da ita, da kuma sauran sakonnin da baka bukata.
To amma wani hanzari ba gudu ba, matsala guda daya tak da ke hana mutane aiwatar da wannan tsarin ita ce, wannan tsarin zaya yi blocking duk wasu sakonni da zasu iya zuwa daga wasu lambobi na musamman. Wannan yana nufin cewa mutum zaya iya rasa samun muhimman sakonni masu matukar muhimmaci a gareshi, misali sakonnin banki (wato Bank Alert) da dai sauransu.
A cikin wannan kasidar tamu ta yau, mun kawo muku cikakken bayani akan yanda zaku iya zabar ire-iren sakonnin da kuke bukatar karba tare da yin blocking din sauran sakonnin wadannan baku bukata.
Kamar dai yanda kuka sani, domin tsaida karbar sakonnin da ke zuwa daga wasu lambobi na musamman, mutum zaya aika da sakon STOP zuwa ga 2442 . Ko wane irin kalar sako da ke shigo maka yana da wata lamba ko kuma code na musamman da ake amfani wajen gane irin sakon. Misali akwai sakonni irin na Bank , Tallace-tallace ,
CallerTune, Labarai da dai sauransu. Ko wane daga cikin wadannan ire-iren sakonnin yana da lambarshi.
Bayan ka aika da sakon STOP zuwa 2442 , domin zabar ire-iren sakonnin da kake bukatar su rika shigo maka, sai ka duba wannan jerin da muka kawo kamar:
1. Ka tura 1 zuwa 2442 domin samun sakonni daga bankinka (kamar irin Alert da sauransu)
2. Ka tura 3 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harkar ilimi (wato Education)
3. Tura 4 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harka lafiya (wato Health)
4. Tura 5 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harkar tallace-tallacen hajoji
5. Tura 7 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harka yawon bude ido (wato Tourism)
6. Tura 8 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harka wasanni (wato Sports)
7. Tura 9 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi harka addinai (wato Religion)
8.Tura 10 zuwa 2442 domin samun sakonni daga gidan layinka
9. Tura 11 zuwa 2442 domin samun sakonni da suka shafi labarum duniya (wato News)
10. Idan kuma kana bukatar gane cewa ko lambar na cikin wannan tsarin, to sai ka tura STATUS zuwa ga 2442 .
A tuna wannan tsari duk daya ne kuma yana aiki akan ko wane irin layin Sadarwa. To mi kuke jira? Ku hanzar domin kare layukanku daga dibar kudi da kuma karbar sakonnin da baku da masaniya akan su.

No comments:
Post a Comment