Sunday, 24 June 2018
Facebook HACKING
FACEBOOK HACKING (KUTSE A FACEBOOK)
A ‘Yan kwanakin nan da muke ciki, yawan matsalar “Hacking” ko kuma yin kutse a Facebook account na mutane, musamman ma ‘yan Nigeria sai kara yawaita yake yi. Sau da yawa wasu mutane kan yi tambaya cewa “Wai shin minene su wadannan masu yin kutse ko kuma “ Hacker ” ke amfanuwa da shi idan suka yin na Facebook Account?
A cikin wannan kasida tamu ta wannan lokaci, zan yi kokarin fayyace muku wannan matsalar tare da kawo dalilan da ya sanya “ Hackers ” ke yin hacking na Facebook account, da kuma hanyoyin da zaku iya bi domin kare kanku daga shiga hannun wadannan miyagun “ Hackers” .
Wasu mutane na ganin cewa, kafafen sada zumunta (kamar su Facebook), ba wasu wurare ba ne da mutum zaya iya adana wasu muhimman bayanai nasa, to don haka babu bukatar damuwa sosai akan tsaro ko kuma security na wannan account din. Amma wadannan mutane basu san ba cewa, wadannan bayanan da suka raina (kamar su Posting, Likes, Sharing, Hobbies, Friends da dai sauransu) sune abubuwa da wani ke bukatar samu ido rufe domin yayi amfani da su wajen cimma wasu manufofi na sa.
Wasu Karin dalilan da ya sanya ake Hacking Facebook account sun hada da:
1. ZARGI:- Zata iya yiyuwa mace ce ke da saurayi ko kuma Namiji ne ke da budurwa, amma kuma dayansu na zargin daya akan wannan soyayya tasu, to haka zaya iya sanyawa dayansu ya bukaci yin
Hacking na Facebook account din daya domin gane ma idonsa abin da dayan ke aikatawa, domin samun tabbacin abin da yake zarginsa a kai
2. MUGUNTA :- Zata iya yiyuwa wani ne ke son ya goga maka kashin kaji, to zaya so yayi Hacking na Facebook account naka domin yin wani abu na batanci wanda bai dace ba, ta yanda duk wanda ya gani sai ya ce ai kaine ka rubuta hakan. Ko kuma zaya iya yiyuwa Account din na wani babban mutum ne (kamar dan siyasa), to shima zasu so yin Hacking na account din nasa domin ja masa wani sharri
3 .YADA FASADI* :- Akwai wasu mutane da ke son yada wasu abubuwan barna (kamar su Hotuna da Videon batsa), to kasancewar sun san ba kowa ne zaya iya ziyartar shafukansu ba domin kallon wadannan abubuwa, sai su so yin amfani da account na wasu sahihai ko kuma dattijan mutane domin yada wannan abu, ta yanda wanda bai taba ganin irin wadannan abubuwa ba ma zaya iya gani.
Wadannan sune manyan dalilai da ke sanyawa ake yawaita yin Hacking na Facebook din mutane.
Tunanin mutane na cewa, “Ai ba wasu muhimman bayanai ne suke adanawa a ba Facebook, don haka basu bukatar damuwa da tsaro ko kuma security na wannan account na su” shine babban nakasu da wadannan mutane masu hacking facebook account ke amfani da shi domin cimma manufarsu. Domin tabbatar da tsaron Account dinku tare da kuma kare kanku daga shiga hannun wadannan mutane, sai ku yi amfani da wadannan shawarwari kamar haka:
1.Kada ku yi amfani da lambobin wayoyinku a matsayin password :- Wannan na daya daga cikin manyan Dalilan da suka sanya Hacking na Facebook Account ya yawaita a cikin mutanenmu. Mafi yawan mutanen suna tsoron kar su manta, shi yasa suke sanya lambobin wayoyinsu a matsayin password dinsu. Amma hakan ba hujja ba ce domin akwai abubuwa da yawa da zasu iya amfani da su a matsayin password dinsu, wadanda su ma ba zasu manta su ba.
*2.* Ku yi Amfani da password mai Karfi :- Password mai karfi shine password wanda ya hada manyan baki (capital letters), kananan baki (small letters), lambobi da kuma alamomin rubutu (punctuations). Irin wannan password zaya yi matukar wuya wani ya iya hacking dinsa
3. Kar ku baiwa wani mutum bayananku na sirri :- Wasu mutane basu san cewa za’a iya amfani da bayanansu na sirri ba, kamar su ranar haihuwa, sunan garin da mutum yake, lambar waya, email address da dai sauransu, wajen yin hacking na Facebook. A duk lokacin da zaku bada wadannan bayanan, to ku san wanda zaku baiwa.
*4*. Kar ku fadawa kowa code din da Facebook suka turo muku :- Wasu Hackers din kan yi kokarin canja password din mutum, to kuma saninku ne cewa idan mutum zaya canja password sai Facebook sun tura masa wasu lambobi a wayarsa domin tabbatar da cewa shine mai account din. Wasu na amfani da wannan dama, sai su bugo ma mutum waya cewa sun yi kuskure wajen saka lamba, ya taimaka ya basu code din da aka turo Da kun kuskura kun basu wannan code din, to fa ta account dinku ta kare .
*5.* Ku yi amfani da “2 Factor Password ” :- “2 Factor Password” wata sabuwar dubara ce da Facebook suka bullo da ita, ta yanda mutum zaya iya zabar
devices (ko browsers) din da za’a iya hawa Facebook dinsa ta hanyar su (misali wayarka da computarka), a duk lokacin da aka so yin login a cikin account dinka ba daga wadannan amintattun devices da ka zaba, to sai an sanar da kai tare da bukatar ka sanya wani code idan har kai ne ke bukatar shiga account din daga wannan browser (ko kuma device).
Daukar dukkanin wadannan matakai da muka kawo, tare da amfani da shawarwarin da muka baku a cikin wannna kasidar, zaya taimaka muku matuka wajen kare kanku daga shiga hannun miyagun “ Hackers” da a ko da yaushe kokarinsu shine su tsawwala ma mutane.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)

No comments:
Post a Comment