Monday, 11 February 2019

MY LOCATIONS






Da yawan mutane suna siyan wayoyin hannu ne ba don abunda wayoyin suka kunsa ba (facilities) sai don ado ko burgewa. Wani har ya jima da wayar tasa baya iya sanin wata bukata ta musamman da wayar zata iya yi masa a al'amuran sa na yau da gobe. Waya ta shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan Adam har da tsaron rayuka da gujewa fadawa hadari kamar kidnapping. Da yawan mutane suna amfani da applications na wayoyin su amma basu gama kewayewa da abubuwan da wannan applications zasu amfane su ba.



Wani zai iya tambayar kan sa ta yaya zan iya maganin kidnapping ko satar mutum ta hanyar amfani da wayar hannu? Wannan abu ne mai sauki kuma mai saukin ganewa. A yanzu mafi yawan masu amfani da wayoyi suna yin watsapp. Ta hanyar amfani da watsapp zaka iya maganin kidnapping ko da anyi kidnapping naka za'a iya gane a inda kake cikin sauki. Yadda zaka yi hakan shine:

1. Ka kunna "location" na wayar ka.
2. Ka shiga watsapp application ka zabi wanda kake so ka yiwa sharing location dinka.
3. A kasa, inda kake sharing hotuna zaka ga option na "location" sai ka shiga zaka ga yana detecting current location din kake a wannan lokacin. Bayan ya gama zai nuna maka unguwar da kake a map.

Daga nan kana da zabi guda biyu. Zaka iya sending current location din da kake ko kuma kayi sharing live location. Banbancin na farko da na biyun shine:

Sending current location: shine ka turawa wani inda kake a wannan Lokaci. Wannan zai taimaka idan aka kama mutum baa san inda yake ba. Idan ya turawa wani location din za'a gane wajen da yake ba tare da shan wahala ba.

Sharing live location: in ka zabi wannan kuma, duk wanda ka turawa wannan lokaction din zai rika ganin duk inda kake a map din. Misali ka taho daga Kano, sai ka yiwa wani sharing live location din ka a kaduna, duk inda kake yana gani a nasa map din kuma yana tracing din ka. Wannan zai taimata shima wajen gane inda mutum yake. Zai fi taimakawa jami'an tsaro wajen sanin matakin da zasu dauka. Amma kai zaka fara taimakawa kan ka duk sanda zaka yi tafiya mai tsayi kayi sharing live location din ka da wani a wani garin don gudun faruwar wani abu mai kama da kidnapping.

Ina fatan mutanen mu zasu fara amfani da wannan dabara. Shi watsapp ba wai iya chatting kawai ake ba harda irin wadannan muhimman al'amura wadanda suke taimakawa tsaron rayuwa da dukiyoyin al'umma.

Monday, 31 December 2018

FIND MY ANDROID

              Sabuwar hanyar find my Android 




Kamfanin gooogle ya yunkuro da wata sabuwar hanyar magance bacewar wayiyin tafida gidanka wato androids phones wannan ba wani abubane illa  saka wata kalma mai suna find my android a cikin shafin su na google
.
Wannan kalmar ita ce mutum zai yi amfani da ita a lokacin da yake neman wayarsa, ko ta wurin tunanin wani ya ɗauke ta, ko kuma ta hanyar neman ta domin rashin sanin inda ya saka ta.
Kamfanin wanda suka haɗa wannan tsari da tsarin da suke da shi na Android DeviceManager yana baka damar gann cewar wayar tana kusa da shi.
Wani ƙarin abin jin daɗi shi ne, shi wannan tsari zai buɗe maka taswirar wurin da wayar take (Map) ta amfani da google Map, ya nuna maka daidai inda wayar take a yanzu, ko kuma lokaci na ƙarshe da google ya sami labarin inda wayar take.
Abubuwan da mutum yake buƙata a wannan tsari shi ne mallakar gmail account,saboda haka INA mai shawar duk Wanda yakaranta wannan kasidar to yayi kokarin bude gmail account saboda muhimmancinsa .

TO YAYA FIND MY ANDROID YAKE AIKi







 shi wannan tsari zai buɗe maka taswirar wurin da wayar take (Map) ta amfani da google Map, ya nuna maka daidai inda wayar take a yanzu, ko kuma lokaci na ƙarshe da google ya sami labarin inda wayar take My Android: Ba manhaja ba ce, kamar yadda aka saba a baya cewar manhajojin da suke iya gano waya idan ta ɓace za ka ga manhaja ce. Find My Android tsarin bincikene da kamfanin google ɗin suka ƙara a cikin surkullen binciken su. Misali idan mutum yana neman abu a intanet zai shiga browser kawai ya buɗe shafin google ya rubuta abin da yake nema, idan sakamako ya fito sai mutum ya zaɓi wanda ya fi dacewa da shi ya buɗe shi
.
To shi ma wannan tsarin neman wayar kusan haka yake, idan kana neman wayarka abin da za ka yi sai ka nemi kwamfuta ko waya mai intanet ka buɗe browser sai ka rubuta www.google.com idan shafin ya buɗe sai ka yi sign in da imel ɗinka na gmail.hafin google a lokacin da ka rubuta www.google.com

[blockquote]Wannan imel da za ka yi amfani da shi ka tabbatar da cewar shi ne wanda kake amfani da shi lokacin da wayar take tare da kai. Da shi kake saukar da manhajoji da suke Google Play Store. Kasancewar duk abin da kake yi da wannan wayar gidan google suna lura da shi
Idan shafin ya karɓi abubuwan da ka saka na username da password sai ka dawo ramin da aka ajiye domin yin binciken abubuwa a google sai kawai ka rubuta Find My Android. Wannan shi ne kawai abin da za ka rubuta, da zarar ka gama rubutawa sai ka latsa maɓallin google search daga nan google zai fara bincikar inda ya ga wayar ɗazu ko kuma yanzu.  
YA GOOGLE YAKE IYA GANO TA?
Kamfanin google suna amfani da abubuwa guda biyu wanda duk wayar-tafi-da-gidanka tana tare da su, Intanet da GPS. Duk wayar da aka ce Smartphone (wayar-tafi-da-gidanka ) ce to za ka samu tana yin browsing wanda shi ne ma dalilin da ya sa mutane suke son amfani da wayar. Global Positioning System (GPS) wata na’ura ce da ake amfani da ita wurin gano wurin da abu yake ta hanyar amfani da ilimin sanin wuri na Longitute da Latitude. Wannan na’ura ma’aikatu da dama suna amfani da ita, musamman masu fitar da filaye, ko taswirar garuruwa, ko masu neman faɗin wuri kamar masu aiki Ƙasa da Safiyo da dai makamanta su. To kusan dukkan wayoyin-tafi-da-gidanka suna da wannan na’ura ta GPS a cikinsu, wanda shi ne, mutane ke amfani da shi a Google Map wurin yin tafiya don gano wurin da mutum bai sani ba, ko kuma domin fahimtar adireshin da wani wuri yake.
Tun da wayoyin wannan lokaci suna amfani da Intanet da GPS sai kamfanin google suke yin amfani da wannan dama su gano wurin da wayar take.

ME ZAN IYA YI IDAN NA GA WAYAR TAWA?

Idan aka yi sa’a wanda ya tsinci wayar ya kunna intanet, to da zarar ka neme ta zai nuna maka wurin da take, idan kuwa a daidai lokacin da kake neman ta ba ta kan intanet to google zai nuna maka wuri na ƙarshe da lokacin da aka shiga intanet da ita.
Abubuwa guda uku zaka iya yi da wayar
  1. Kiranta: Da farko za ka iya sagoogle su kira wayar (ringing) wanda idan kana tunanin ba dauke maka ita aka yi ba, ka rasa inda ta shiga ne, kuma ba ka da wayar da za ka kira amma kuma ga kwamfuta mai intanet a wurin.
  2. Kulle Ta: Za ka iya rufe wayar yadda ba wanda zai iya amfani da ita. A lokacin da kake ƙoƙarin shirya yadda kake son wayar ta rufe, za ka cike wani ɗan ƙaramin fom da googleza su ba ka wanda za ka rubuta kalaman sirri da kake son ayi amfani da su wurin buɗe wayar (password), domin idan an kulle ta kuma aka ganta ba sai kayi amfani da intanet ba wurin buɗe ta ba. Sannan zaka rubuta saƙon da kake son wanda ya buɗe ita wayar ya gani misalin kamar ka rubuta “Wannan wayar an sace ta ne”. Daga ƙarshe sai ka sa lambar wayar wanda kake son a kira idan an tsinci wayar.
Wannan shi ne abu na biyu da mutum zai yi, yin haka zai kulle wayar duk lokacin da aka buɗe intanet ɗinta. Kuma ko da mutum ya yi factory reset, wato ya goge wayar ta dawo kamar ranar da aka sayeta, da zarar ta ji ƙanshin intanet za ta sake kulle kanta.
  1. Goge ta: Abu mafi muni da mutum zai yi shi ne ya goge wayar gaba ɗayan ta, ta hanyar lalata dukkan abin da ke cikinta. Ba ana maganarcontact da saƙonni ba ne, wannan tsarin zai baka damar goge wayar ce baki ɗayanta, ta hanyar goge manhajar wayar gaba ɗaya yadda wayar har abada ba zata yi amfani ba.
Wannan shine tsarin da kamfanin google suka ɓullo da shi domin magance masu satar wayar Android.
HAVE A QUESTIONS,? COMMENTS BELOW
THANKS.............

Friday, 9 November 2018

TRCN

11,550 Pass Professional Qualifying Exam For Teachers As 5,405 Fail -TRCN



The Teachers Registration Council of Nigeria (TRCN) says 11,550 candidates passed the Professional Qualifying Examination (PQE) for teachers, representing 68 per cent of the total number of candidates.
‎The Registrar of TRCN, Professor Josiah Ajiboye, who  said this in an interview in Abuja on Friday, however, said that 5,405 candidates failed the examination.
The October diet of P‎QE, which is the second in the year, was written between October 19 and 20 nationwide.
Ajiboye said that a total of 18,647 candidates registered for the examination but only 16,955 candidates sat for the examination.
“The total number of candidates who sat for the examination was 16,955, out of which‎ 11, 550 passed; representing 68.12 per cent of the total number of candidates that sat for the examination.
“On the other hand, 5,405 candidates failed the examination, and the figure represents 31.88 per cent of the total number of those who wrote the examination.
“The ‎ results have been ‎approved by the management of the Teachers Registration Council of Nigeria for onward transmission to State/FCT Coordinators for immediate release,’’ he added.
The registrar noted that the conduct of the examination across the country was hitch-free, adding that those who failed the exam would have another opportunity to rewrite it next year.

Ajiboye said that the examination ‎covered every subject which qualified a person to be a good teacher.
“The examination covered areas such as basic knowledge of‎ principles and practice of education, psychology, philosophy and the pedagogical skills which one needs to be a teacher‎.’’
‎Ajiboye, however, warned that by December 2019, any teacher who was not qualified, registered and licensed by the council would no longer be allowed to teach in any school across the country ‎.
“That date is sacrosanct; that is the date that has been approved by the National Council on Education, which is the highest decision-making body on education in Nigeria,’’ he said.

Thursday, 11 October 2018

GARABASAR AIRTEL

A kokarinmu na kawo muku hanyoyi masu sauki wajen samun data kyauta, a yau ma mun kawo maku wata hanyar da zaku samu wannan datar mai yawa wacce takai 1GB acikin sauki, kuma wanna datar tana daukar tsawon kwana 30.

To wadanne matakaine akebi!?

1 katabbatar Kannada layin zain( airtel)

ka danna *479# said ka kira

Sunday, 2 September 2018

GARABASA!!!

                                                      MTN FREE BROWSING!!!!

                           Kamfanin layin waya na MTN ya samar da wata gagarumar dama da mutane zasu iya samun kyautar datar da zasu iya amfani da ita wajen shiga ko wane lungu da sako na kafar sadarwar Internet. Wannan garabasa dai a bude take ga duk wani mai amfani da layin MTN, ba kamar sauran bonanza da akan ce dole sai wasu tsirarun mutane masu amfani da wani tsari na musamman.
Ita dai wannan garabasa ta samo asali ne daga kyautar data da MTN suke baiwa duk wanda yayi intsalling na wani application na su mai suna MyMTN App . Shi dai wannan app yana baiwa mutum dama yayi duk wasu abubuwan da ya shafi layin MTN kamar sanya kati, siyen kati daga banki, tura sakonni, warware wata matsala da mutum ke fama a ita da dai sauransu.
Kai tsyaye domin samun wannan garabasa, sai ku bi wadannan ‘yan matakan kamar haka:

1. Ku yi download na MyMTN App (Zaku iya samun sa a Play Store)

2. Ku yi installing na app din a cikin wayarku ta android

3. Ku shiga cikin app din (amma sai kun buda datarku ta MTN, ko da kuwa babau datar a 
ciki). In kun shiga zaya nuno muku jerin kasashe, sai ku zabi kasarku kamar haka:

4. Bayan kun zabi kasarku abu na gaba shine, zaku jira app din ya gama loading.

 Da zaran ya gama loading zaku ga ya nuno muku wani page. Idan kuka duba a saman wannan page da ya buda zaku ga sun numa muku cewa, kun samu nasarar samun 500MB ta kyauta. Sai ku taba rubuta domin karbar wannan MB da suka baku!

Idan kuna son samun sama da 500MB , zaku iya mai-maita wannan matakan akan wasu layukan naku. 

Idan kuna da layi guda 10, zaku iya mai-maita wannan a kansu kun ga ke nan zaku samu datar da yawanta ya kai 10GB . Amma ku tabbatar layin da zaku yi mawa yana cikin wayarku, ko kuma wayar da yake cikinta tana kusa da ku, domin zasu turo wani code ta cikin layin sai ku sanya a cikin app din kafin su baku.

A kula: Wannan data za’a yi amfani da ita a rana daya kacal!

Idan kunada wata matsala wajen bude wannan, yi comments  a kasa

Sunday, 24 June 2018






LOAPI VIRUS!

Masu bincike akan harkar tsaro ko kuma security na  computer, sun binciko wata sabuwar Virus da ke kama wayoyi  kirarAndroid. Wannan sabuwar Virus ana kiranta da “Loapi” virus, kuma tana da matukar hatsarin gaske.
Ita dai wannan Virus ta fara baiyanuwa  a cikin wannan makon, kuma ya zuwa yanzu ta kama dubban wayoyin kirar android.  Masu bincike a kamfanin nan da ya kware a fagen samar da Antivirus mai suna Kaspersky, su ne suka bayyana labarin gano wannan Virus. Wadannan masu bincike sun bayyana wannan Virus a matsayin wata abu da da za’a iya alakantawa da “komi da ruwanka” domin kusan duk wata barna da aka sani Virus na yi a cikin wayoyin android, to ita ma wannan Virus tana yinsu.
Ita wannan Virus idan ta kama waya to zata sanya duk wasu application da ke cikin wayar su bar aiki tare da yi ma wayar rooting, a lokaci guda kuma ta rika zuke wuta ko kuma power din wayar, wannan kan sanya wayar dau zafi sosai ta yanda kai tsaye batirin kan iya mutuwa ko kuma wayar ta yi bindiga!
Akwai wasu muhimman aiyuka da wannnan Virus ke tilastawa waya yinsu. Wadannan ayyuka sun hada da:
1.      Hakar kudin sama (wato Bitcoin mining), ta yanda masu ita zasu samu wadannan kudaden
2.      Yin amfani da wayar domin yin hacking din wata computer, ta yanda ko da aka yi binciken wanda yayi hacking din, to sunan mai wayar za’a gani a maimakon su hackers din
3.      Sanya tallace-tallace masu yawa a kan screen
4.      Yin leken asiri akan sakonnin mutum (SMS)
Wadannan muhimman aiyuka da wannan Virus ke sanyawa waya na yi duk a cikin lokaci daya, su ke sanya wayar ta dauki zafi sosai har ma batirin ya iya yin binda.
Wasu dubaru da masu wannan Virus din ke amfani da su domin yaudarar mutum yayi installing wannan App na su sun hadIa da nuna wannan App din a matsayin wani app mai dauke da hotunan banza, da kuma sanya App yayi kamanceceniya wasu application da aka fi amfani da su.
TA YAYA ZAKU IYA KAREN KANKU DAGA “LOAPI” VIRUS?
Idan wannan Virus bata kama wayarku ba, to abin da zaku yi domin kare kanku shine kada ku sake ku yi installing wani application da bai fito daga sahihin wuri ba (misali Play Store).
Idan kuma an samu rashin sa’a wannan Virus ta kama wayarku, to abin yi shine kawai mutum yayi kokarin zare batirin wayar zuwa wani lokaci, tare da yin wiping ko kuma goge abubuwan da cikinta gaba daya!
Da fatan za’a kula sosai domin kare kai daga wannan hatsabibiyar Vitus

Facebook HACKING

                           
                                 FACEBOOK HACKING (KUTSE A FACEBOOK)

A ‘Yan kwanakin nan da muke ciki, yawan matsalar “Hacking” ko kuma yin kutse a Facebook account na mutane, musamman ma ‘yan Nigeria sai kara yawaita yake yi. Sau da yawa wasu mutane kan yi tambaya cewa “Wai shin minene su wadannan masu yin kutse ko kuma “ Hacker ” ke amfanuwa da shi idan suka yin na Facebook Account?

A cikin wannan kasida tamu ta wannan lokaci, zan yi kokarin fayyace  muku wannan matsalar tare da kawo dalilan da ya sanya “ Hackers ” ke yin hacking na Facebook account, da kuma hanyoyin da zaku iya bi domin kare kanku daga shiga hannun wadannan miyagun “ Hackers” .
Wasu mutane na ganin cewa, kafafen sada zumunta (kamar su Facebook), ba wasu wurare ba ne da mutum zaya iya adana wasu muhimman bayanai nasa, to don haka babu bukatar damuwa sosai akan tsaro ko kuma security na wannan account din. Amma wadannan mutane basu san ba cewa, wadannan bayanan da suka raina (kamar su Posting, Likes, Sharing, Hobbies, Friends da dai sauransu) sune abubuwa da wani ke bukatar samu ido rufe domin yayi amfani da su wajen cimma wasu manufofi na sa.
Wasu Karin dalilan da ya sanya ake Hacking Facebook account sun hada da:

1. ZARGI:- Zata iya yiyuwa mace ce ke da saurayi ko kuma Namiji ne ke da budurwa, amma kuma dayansu na zargin daya akan wannan soyayya tasu, to haka zaya iya sanyawa dayansu ya bukaci yin
Hacking na Facebook account din daya domin gane ma idonsa abin da dayan ke aikatawa, domin samun tabbacin abin da yake zarginsa a kai


2. MUGUNTA :- Zata iya yiyuwa wani ne ke son ya goga maka kashin kaji, to zaya so yayi Hacking na Facebook account naka domin yin wani abu na batanci wanda bai dace ba, ta yanda duk wanda ya gani sai ya ce ai kaine ka rubuta hakan. Ko kuma zaya iya yiyuwa Account din na wani babban mutum ne (kamar dan siyasa), to shima zasu so yin Hacking na account din nasa domin ja masa wani sharri


3 .YADA FASADI* :- Akwai wasu mutane da ke son yada wasu abubuwan barna (kamar su Hotuna da Videon batsa), to kasancewar sun san ba kowa ne zaya iya ziyartar shafukansu ba domin kallon wadannan abubuwa, sai su so yin amfani da account na wasu sahihai ko kuma dattijan mutane domin yada wannan abu, ta yanda wanda bai taba ganin irin wadannan abubuwa ba ma zaya iya gani.
Wadannan sune manyan dalilai da ke sanyawa ake yawaita yin Hacking na Facebook din mutane.
Tunanin mutane na cewa, “Ai ba wasu muhimman bayanai ne suke adanawa a ba Facebook, don haka basu bukatar damuwa da tsaro ko kuma security na wannan account na su” shine babban nakasu da wadannan mutane masu hacking facebook account ke amfani da shi domin cimma manufarsu. Domin tabbatar da tsaron Account dinku tare da kuma kare kanku daga shiga hannun wadannan mutane, sai ku yi amfani da wadannan shawarwari kamar haka:
 1.Kada ku yi amfani da lambobin wayoyinku a matsayin password :- Wannan na daya daga cikin manyan Dalilan da suka sanya Hacking na Facebook Account ya yawaita a cikin mutanenmu. Mafi yawan mutanen suna tsoron kar su manta, shi yasa suke sanya lambobin wayoyinsu a matsayin password dinsu. Amma hakan ba hujja ba ce domin akwai abubuwa da yawa da zasu iya amfani da su a matsayin password dinsu, wadanda su ma ba zasu manta su ba.
*2.* Ku yi Amfani da password mai Karfi :- Password mai karfi shine password wanda ya hada manyan baki (capital letters), kananan baki (small letters), lambobi da kuma alamomin rubutu (punctuations). Irin wannan password zaya yi matukar wuya wani ya iya hacking dinsa
3. Kar ku baiwa wani mutum bayananku na sirri :- Wasu mutane basu san cewa za’a iya amfani da bayanansu na sirri ba, kamar su ranar haihuwa, sunan garin da mutum yake, lambar waya, email address da dai sauransu, wajen yin hacking na Facebook. A duk lokacin da zaku bada wadannan bayanan, to ku san wanda zaku baiwa.
*4*. Kar ku fadawa kowa code din da Facebook suka turo muku :- Wasu Hackers din kan yi kokarin canja password din mutum, to kuma saninku ne cewa idan mutum zaya canja password sai Facebook sun tura masa wasu lambobi a wayarsa domin tabbatar da cewa shine mai account din. Wasu na amfani da wannan dama, sai su bugo ma mutum waya cewa sun yi kuskure wajen saka lamba, ya taimaka ya basu code din da aka turo Da kun kuskura kun basu wannan code din, to fa ta account dinku ta kare .
*5.* Ku yi amfani da “2 Factor Password ” :- “2 Factor Password” wata sabuwar dubara ce da Facebook suka bullo da ita, ta yanda mutum zaya iya zabar
devices (ko browsers) din da za’a iya hawa Facebook dinsa ta hanyar su (misali wayarka da computarka), a duk lokacin da aka so yin login a cikin account dinka ba daga wadannan amintattun devices da ka zaba, to sai an sanar da kai tare da bukatar ka sanya wani code idan har kai ne ke bukatar shiga account din daga wannan browser (ko kuma device).
Daukar dukkanin wadannan matakai da muka kawo, tare da amfani da shawarwarin da muka baku a cikin wannna kasidar, zaya taimaka muku matuka wajen kare kanku daga shiga hannun miyagun “ Hackers” da a ko da yaushe kokarinsu shine su tsawwala ma mutane.