LOAPI VIRUS!
Masu bincike akan harkar tsaro ko kuma security na computer, sun binciko wata sabuwar Virus da ke kama wayoyi kirarAndroid. Wannan sabuwar Virus ana kiranta da “Loapi” virus, kuma tana da matukar hatsarin gaske.
Ita dai wannan Virus ta fara baiyanuwa a cikin wannan makon, kuma ya zuwa yanzu ta kama dubban wayoyin kirar android. Masu bincike a kamfanin nan da ya kware a fagen samar da Antivirus mai suna Kaspersky, su ne suka bayyana labarin gano wannan Virus. Wadannan masu bincike sun bayyana wannan Virus a matsayin wata abu da da za’a iya alakantawa da “komi da ruwanka” domin kusan duk wata barna da aka sani Virus na yi a cikin wayoyin android, to ita ma wannan Virus tana yinsu.
Ita wannan Virus idan ta kama waya to zata sanya duk wasu application da ke cikin wayar su bar aiki tare da yi ma wayar rooting, a lokaci guda kuma ta rika zuke wuta ko kuma power din wayar, wannan kan sanya wayar dau zafi sosai ta yanda kai tsaye batirin kan iya mutuwa ko kuma wayar ta yi bindiga!
Akwai wasu muhimman aiyuka da wannnan Virus ke tilastawa waya yinsu. Wadannan ayyuka sun hada da:
1. Hakar kudin sama (wato Bitcoin mining), ta yanda masu ita zasu samu wadannan kudaden
2. Yin amfani da wayar domin yin hacking din wata computer, ta yanda ko da aka yi binciken wanda yayi hacking din, to sunan mai wayar za’a gani a maimakon su hackers din
3. Sanya tallace-tallace masu yawa a kan screen
4. Yin leken asiri akan sakonnin mutum (SMS)
Wadannan muhimman aiyuka da wannan Virus ke sanyawa waya na yi duk a cikin lokaci daya, su ke sanya wayar ta dauki zafi sosai har ma batirin ya iya yin binda.
Wasu dubaru da masu wannan Virus din ke amfani da su domin yaudarar mutum yayi installing wannan App na su sun hadIa da nuna wannan App din a matsayin wani app mai dauke da hotunan banza, da kuma sanya App yayi kamanceceniya wasu application da aka fi amfani da su.
TA YAYA ZAKU IYA KAREN KANKU DAGA “LOAPI” VIRUS?
Idan wannan Virus bata kama wayarku ba, .
Idan kuma an samu rashin sa’a wannan Virus ta kama wayarku, to abin yi shine kawai mutum yayi kokarin zare batirin wayar zuwa wani lokaci, tare da yin wiping ko kuma goge abubuwan da cikinta gaba daya!
Da fatan za’a kula sosai domin kare kai daga wannan hatsabibiyar Vitus
No comments:
Post a Comment