MATAKAN DA AKE BI WAJEN KOYON COMPUTER A SAUKAKE
Kasancewar a yanzu computer ta shafi fannoni da dama, wanda kuma wasu daga cikin wadannan fannonin suma sun kasu ya zuwa wasu fannonin, ba zaya taba yiyuwa ba mutum ya iya koyon duk wani ilimi na computer. Ga dukkan mai son samun nasara akan koyon ilimin computer, to ya zama wajibi ya bi wadannan matakan da zan kawo kamar haka:
1. Zaben Fannin da ake bukatar neman ilimi ko kuma kwarewa a kai
Kasancewar fannonin computer suna da yawan gaske, abin da mutum ya kamata ya fara yi shine, ya fara zabar fannin da yake bukatar samun kwarewa a kai. Yin haka shine abin da zaya ba mutum damar ajiye hankalinsa a waje guda, tare da koyon abin da ya kamata a cikin dan kankanen lokaci. Mutane da yawa kan bijiro da aniyarsu ta koyon ilimin computer ne a lokacin da bukatar yin hakan ta taso, ko dai saboda an bukace su da su yi hakan ne a a wajajen aiyukansu ko kuma saboda sha’awar ilimin computer da suke yi. Akwai bangarorin ilimin computer da dama da mutum zaya iya koyo tare da samun kwarewa a kai. Wadannan bangarori sun hada da Graphic design (yanda ake gyara hotuna da videos) , word document (Yanda ake rubuta ko kuma typing) , Spreadsheet , Presentation, Web design , programming (Yanda kae hada applications na waya da computer) , harkar kasuwanci a internet (wato Digital marketing a turance) da dai sauran dubban ilimummuka da suka shafi bangarori da dama na computer. Tabbas mutum zaya iya samun kwarewa a kan sama da abu daya da ya shafi computer, sai dai abin da ya kamata mutum yayi shine, ya tabbatar ya dauki abu daya a lokaci guda, ba ya dauki abubuwa da dama ba a lokaci guda kuma ya ce yana so ya koye su duk a lokacin, wannan baya yiyuwa! Saboda a karshe mutum zaya kasance bai samu kwarewa a kan ko daya daga cikin fannonin ba.
2. Wajen Da mutum zaya iya neman wannan ilimi a saukake
Mafi yawancin mutanenmu a yanzu abin da suka dauka shine, dole ne sai ka je makarantar computer ka yi certificate kafin ka iya koyon ilimin computer. Eh tabbas akwai wasu fannoni da mutum dole said yaje makaranta, amma yawancin fannoni ba sai kaje makaranta ba. A yayin da wasu mutanen kan bata lokutansu a internet wajen yin abubuwan da ba zasu taba amfanarsu ba (misali chatting da kuma download na abubuwan da ba zasu amfane su ba), wasu mutanen kuma sun maida internet wata makaranta ta musamman inda suke samun ilimi a kan dukkan wani abu da ya shige masu a duhu. Akwai shafukan internet da yawa da mutum zaya iya zuwa domin koyon wani ilimi na computer da ma wasu sauran ilimummuka. Babba daga cikin wadannan shafuka shine Google . A duk lokacin da kake bukatar samun Karin bayani akan wani abu, to da zaran ka sanya wannan abin tare da nemo shi a google, zaka samu sakamako na shafuka da dama da suka yi sharhi akan wannan abin da kake neman bayani ko kuma sani a kansa. Kasancewar wasu mutane sun fi gane abu idan suna kallon yanda ake yin shi kai tsaye, zaku iya amfani da kafar YouTube domin samun video tutorials a kan ko wane abu da mutum ke bukatar koyo. Baya ga wannan kuma, zaku iya kulla mu’amala da mutanen da kuka san suna da masaniya kan wannan fannin da kuke neman ilimi akai, domin zasu iya taimaka maku a yayin da kuke bukatar neman taimako akan wani abu da ya kakare muku.
Baya ga google kuma, akwai website da dama da ke gabatar da kwasa-kwasai daba-daban a kan harkar computer, wasu kyauta ne, wasu kuma ana dan biyan wani abu, amma dai abin da ake biya ko kadan bai kai kudin da mutum zaya kashe a wajen halarta wata makarantar computer ba.
3. Mallakar kayan aiki
Bayan mutum ya zabi fannin da yake son ya nemi kwarewa a kai, kuma ya san wuraren da zaya je ko kuma ya shiga domin nemo wannan ilimi, abu na gaba shine ya mallaki kayan aikin da zaya iya bukata a lokacin da yake neman wannan ilimi. Misali mutumen da yake bukatar koyon Graphic design (wato yanda ake gyara hoto da video) to akalla yana bukatar ya mallaki computer da kuma graphic software kamar Photoshop ko kuma CorelDraw. . Wanda kuma yake bukatar ya kware a kan harkar da ta shafi amfani da computer a ofisoshi ko kuma wajen kasuwanci, to shima yana bukatar mallakar computer tare da office suit ko kuma package kamar Microsoft Office, wanda shi kunshi ne da ya kan zo da duk wata software da mutum zaya iya bukata a wannan fannin kamar Word, Excel , presentation da dai sauransu. Ga wanda baya da computer kuma, zaya iya amfani da computocin makaranta, cafĂ© ko kuma idan yana da wani aboki amintacce da ya mallaki computar, to zaya iya amfani da ita domin yin gwaji akan abin da yake koyo. Hasali ma, mafi yawa daga cikin wayoyin hannu na zamani da muke da su, za’a iya amfani da su wajen koyon kusan duk wani abu da mutum ke bukatar koyo. Mafi sahihancin hanya da mutum zaya auna fahimtarsa akan wani abu da ya koya shine ta hanyar aiwatar da duk abin da ya koya a aikace, ba wai kawai ya karanta ba.
Wadannan matakan sune in dai har mutum ya dauke su, to zaya iya koyon ko wane ilimi yake bukatar koya a fannin computer a saukake ba wai dole sai ya je makarantar computer ba.

No comments:
Post a Comment